PSG ta casa Chelsea 3-1

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Chelsea na bukatar rama kwallaye biyu kafin ta cigaba a gasar

Paris St-Germain ta casa Chelsea da ci 3-1 a karon farko na wasan dab da na kusa da karshe na gasar Zakarun Turai.

Ezequiel Lavezzi ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea minti uku da shiga fili.

Can a minti na 27 Eden Hazard ya rama da bugun daga kai sai me tsaron gida bayan an yi wa Oscar keta.

David Luiz ya ci kansu da kansu minti na 61 bayan Cavani ya kwararo wata kwallo a bugun tazara daga gefen hagu.

Ana shirin tashi a minti na 90 Javier Pastore ya wujijjiga 'yan bayan Chelsea ya kara musu ta uku.

A ranar Talata ta mako me zuwa, takwas ga watan Afrilu za a yi karo na biyu na wasan a gidan Chelsea.

Karin bayani