'Yan wasan West Brom sun yi fada

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Saido Berahino na ganin West Brom ba ta yi hukuncin da ya dace ba.

Dan wasan West Brom Saido Berahino yana duba yuwuwar gurfanar da James Morrison na kungiyar tasu gaban shari'a saboda naushinsa da yayi.

Dan wasan na Ingila na tawagar 'yan kasa da shekara 21 ya ji rauni a fuskarsa sakamakon rikicin da suka yi a dakin sauya kaya bayan wasansu da Cardiff da suka tashi 3-3 ran Asabar.

Kungiyar ta West Brom dai ba ta dauki wani mataki kan 'yan wasan ba sakamakon rikicin da suka yi.

Dan wasan me shekaru 20, da ya ci kwallaye goma a wasanni bakwai da ya yi wa West Brom da Ingila a bara, sau uku kawai sabon kociyan klub din Pepe Mel ya sa shi wasa.

Shi kuwa Morrison, dan wasan da yafi kowa dadewa a West Brom ya yi wa kungiyar wasanni 198 tun da ya dawo daga Middlesbrough a 2007 kan fan 1.5.

Morrison dan Scotland sau 29 ya yi wa kungiyar wasa a bana.