PSG na da sauran aiki- Mourinho

Image caption Mourinho na ganin 'yan wasansa za su iya hana cin duka kwallaye ukun

Kociyan Chelsea Jose Mourinho ya ce PSG ta kwana da sanin cewa da sauran aiki a gabanta duk da casa kungiyarsa da ta yi 3-1.

Mourinho ya kushe salon da 'yan wasansa suka bi na kariya tare da sukn 'yan wasans na gaba bayan PSG ta yi galaba kansu a wasan dab da na kusa da karshe na Zakarun Turai karon farko.

Kociyan ya ce, ''ban ji dadin 'yan wasana na gaba ba ko kadan, dole sai na sake dabara.''

Ya kara da cewa, ''cin kwallo shi ne abu mafi muhimmanci a wasan kwallon kafa. Kuma wannan shi ne aikin 'yan wasan gaba , amma na kwarai. Zan jarraba hakan''

Yayin da kociyan yake yawan sukan 'yan wasansa na gaba, ya ware 'yan bayansa da aka samu cinsu kwallaye hudu kawai kafin wasan na PSG.

Dole ne dai Chelsea ta rama bashin kwallaye biyu da ke tsakaninta da PSG kafin ta cigaba a gasar.

A ranar Talata me zuwa takwas ga watan Afrilu ne za su yi karo na biyu na wasan a gidan Chelsea Stanford Bridge.

Karin bayani