Osaze ya shawarci Berahino ya bar West Brom

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Osaze ya ce, '' ina ganin maimaicin abin da ya faru da ni idan bai bar kungiyar ba.''

Tsohon dan wasan West Brom ya shawarci Saido Berahino ya fice daga kungiyar bayan zargin da ya yi na naushinsa a dakin sa jesi.

Shi dai Saido Berahino ya yi zargin cewa James Morrison dadadden dan wasan kungiyar ya naushe shi a fuska a dakin sa jesi bayan wasansu da Cardiff da suka tashi 3-3 ranar Asabar.

A da dan wasan ya yi nufin kai kara gaban kotu ganin kungiyar ba ta dauki wani mataki akan Morrison ba, amma yanzu an ce ya fasa.

Kan hakan ne Odemwingie me shekaru 32, wanda yake Stoke City yanzu ya ce lamarin ya tuna masa matsalolinsa a West Brom.

Osaze ya ce, '' ina ganin maimaicin abin da ya faru da ni idan bai bar kungiyar ba.''

A lokacin takkaddamarsu, West Brom ta ci tarar dan wasan na Najeriya alawus na sati biyu bayan da ya yi yunkurin komawa QPR ba da izininta ba a watan Janairu na 2013.

Tun daga nan ne kuma suka rinka takun saka da tsohuwar kungiyar tasa.