Matsin lamba na kan City - Rodgers

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Brendan Rodgers

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce matsin lamba na kan Manchester City a hamayyar da suke yi ta lashe gasar Premier a bana.

A mako mai zuwa ne Liverpool za ta karbi bakuncin City a filin Anfield.

A ranar Lahadi Liverpool ta sake darewa kan teburin gasar bayan ta doke West Ham da ci biyu da daya a Upton Park.

Rodgers yace "Matsin lamba na kansu, saboda sun kashe makudan kudade wajen sayen 'yan wasa don lashe gasar Premier da ta Zakarun Turai".

Rabon da Liverpool ta lashe gasar cin kofin Premier tun shekarar 1990.

Karin bayani