Ya kamata Wenger ya tafi -Ian Wright

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ian Wright ya ce, ''idan ka dubi sakamakon Chelsea da Liverpool ka dubi namu, za ka ga kamar 'yan wasan ba a shirye suke ba.''

Tsohon dan wasan gaba na Arsenal Ian Wright na ganin cewa ya kamata nan gaba kadan kociyan kungiyar Arsene Wenger ya kara gaba.

Rabon da kungiyar ta ci wani wasa dai tun ranar 16 ga watan Maris kuma a maki 12 da ta yi hari biyu kawai ta samu kwanakin nan.

Haka kuma damar klub din a gasar Zakarun Turai na cikin hadari bayan da Everton ta lallasa su 3-1 ranar Lahadi.

Wannan hali da Arsenal ke ciki ya sa Ian Wright yake cewa, ''mun doshi shekaru goma ke nan yanzu babu wani kofi da muka dauka.

Kuma babu alamar wani cigaba. Don haka wajibi ne su dau mataki zuwa wani lokaci.

Matakin da zai sauya yanayin kungiyar Arsenal baki daya.''

Tsohon dan wasan ya kara da cewa, ''idan ka dubi sakamakon su Chelsea da Liverpool ka dubi namu, za ka ga kamar 'yan wasan ba a shirye suke ba.''