Chelsea ta kai wasan kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sau biyu Chelsea ta kai wawan hari inda Schurrle da Oscar su ka buga kwallon tana bugun karfen saman raga.

Chelsea ta tsallake rijiya da baya, bayan ta doke PSG 2-0 a Stanford Bridge zuwa wasan kusa da karshe na Zakarun Turai.

A karon farko PSG ta ci Chelsea 3-1 a Paris, da wannan nasarar ta 2-0, jumulla 3-3 ke nan.

Sakamakon kwallon da Chelsea ta jefa a ragar PSG a Paris ta samu galaba.

Andre Schurrle wanda ya shigo daga baya ne ya fara ci wa Chelsea kwallonta a minti na 31.

To amma minti uku ya rage lokaci ya cika na wasan sai Demba Ba ya ceci Chelsea da kwallo ta biyu.

Karin bayani