Real Madrid da fitar da Dortmund

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kafin wasan Real Madrid ce ake ganin za ta sake lallasa Borussia Dortmund amma, kungiyar ta Jamus ta kasance ta fi wasa.

Real Madrid ta kai wasan kusa da karshe na Zakarun Turai bayan ta yi rashin nasara da ci 2-0 a gidan Dortmund, amma da sakamakon wasan farko ta tsira da ci 3-2.

Real Madrid ta barar da damarta a wasan bayan da Angel Di Maria ya kasa cin bugun fanaretin da suka samu tun da farko.

Daga nan ne mai masaukin baki, Dortmund ta samu dama ta jefa kwallonta ta farko ragar kungiyar ta Spaniya ta hannun Reus a minti na Marco 24.

Can kuma bayan mintuna 13 sai Reus din ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar Real Madrid.

Kafin wasan Real Madrid ce ake ganin za ta sake lallasa Borussia Dortmund amma, kungiyar ta Jamus ta kasance tafi taka rawa.