Rooney na shirya wa Bayern Munich

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mun yi imanin za mu iya samun nasara.Muna da isassun 'yan wasa masu kyau, in ji Rooney

Wayne Rooney ya yi atisaye a shirin da kungiyarsa take yi na fafatawa da Bayern Munich na wasan dab da na kusa da karshe karo na biyu ranar Laraba.

Akwai damuwa game da lafiyar dan wasan bayan da ya ji rauni a babban yatsansa na kafa a karon farko a Old Trafford da suka tashi 1-1.

Raunin nasa yasa bai shiga wasan da Manchester United ta yi ba da ta ci Newcastle.

Sai dai kuma kociyan Bayern Munich Pep Guardiola na ganin ba wata shakka Rooney mai shekaru 28 zai yi wasan a Jamus.

Guardiola, ya ce, '' wannan daya ne daga cikin gwanayen 'yan wasan da na gani kuma manyan 'yan wasa ba sa son a bar su a baya a irin wannan wasa.''