Da wuya Sunderland ta tsira - Poyet

Image caption Na dauki alhakin gazawarmu saboda ni ne ke shugabanci in ji Poyet

kociyan Sunderland Gus Poyet ya ce, zai kasance mu'ujiza idan kungiyarsa ba ta fadi daga Premier ba.

Sunderland ta ci gaba da kasancewa ta karshe a tebur bayan da Tottenham ta casa ta 5-1 ranar Litinin.

Gus Poyet wanda ya gaji Paolo Di Canio da aka kora a watan Oktoba, ya ce, ''wani lokacin tebur ba ya karya. Zai zama abin mamaki mu tsira.''

Sauran wasanni bakwai da suka rage wa kungiyar sun hada da na Everton da Cardiff da West Brom da Swansea a gida.

Yayin da za ta je wa Manchester City da da Chelsea da kuma Manchester United.

Poyet na ganin kungiyar tasa na bukatar nasara a akalla wasanni hudu daga cikinsu ta tsira a gasar ta Premier.