Atletico ta yi waje da Barcelona da 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rabon da Atletico ta ci Barcelona shekara hudu, rabon da ta kai wasan kusa da karshe na gasar shekaru 40

Atletico Madrid ta yi waje da Barcelona a gasar Zakarun Turai bayan da ci 2-1 jumulla a wasanni biyu.

A wasan na dab da na kusa da karshe karo na biyu Atleticon sun ci Barcelonan 1-0 ta hannun Koke a minti biyar da fara wasa.

Daman a wasan farko a gidan Barcelona Nou Camp sun tashi kunnen doki ne 1-1.

Cikin mintina 20 na farkon wasan sau uku Atletico na kai hare hare masu hadari kwallon na bugun karfen saman raga .

Karin bayani