Dole Bayern ta doke United - Guardiola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan Bayern Munich

Kocin Bayern Munich, Pep Guardiola ya ce kungiyarsa ba za ta lamunci kasa tsallakewa zuwa wasan karshe a gasar Zakarun Turai ba.

Bayern wacce ke kokarin kare kofinta, za ta dauki bakuncin Manchester United ne kuma a bugun farko sun tashi kunen doki.

Guardiola yace "Idan bamu kai wasan karshe ba, ba zamu lamunta ba".

A kakar wasan da ta wuce Bayern Munich ta lashe kofuna uku wato na zakarun Turai, da na Bundeslisga da kuma na kofin Jamus.

Karin bayani