Hazard zai yi jinyar makonni biyu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Eden Hazard

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce dan kwallonsa Eden Hazard zai yi jinyar akalla makonni biyu.

Dan kwallon Belgium din mai shekaru 23 ya ji rauni ne a wasansu da Paris St-Germain, amma dai Chelsea din ta samu galaba da ci biyu da nema.

Nasarar ta sa Chelsea ta tsallake zuwa zagayen kusa da karshe a gasar zakarun Turai.

Mourinho yace "Matsala ce a kafarsa amma ban san tsananin raunin ba".

Jinyar da Hazard zai yi, za ta sa ba zai buga wasansu da Swansea da kuma Sunderland ba.

Karin bayani