FA ta ki yarda da sauya sunan Hull City

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan kungiyar sun yi murna da hukuncin

Majalisar Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ta ki amincewa da bukatar sauya sunan kungiyar Hull City zuwa Hull Tigers.

Kashi 63.5 cikin dari ne na mambobin majalisar suka ki yarda da bukatar wadda me kungiyar Assem Allam ya gabatar.

Allam mai shekaru 74 wanda ya yi barazanar sayar da kungiyar idan ba a amince da bukatar tasa ba, ya ce zai daukaka kara.

Allam na ganin sunan 'City' ya zama ruwan dare kuma sauya shi da 'Tigers' zai jawo wa kungiyar karin kasuwa.