Pistorious ya ki kallon hoto

Image caption Pistorious ya kafe cewa kan kuskure ya harbe budurwar tasa

Mai gabatar da kara na gwamnatin Afirka ta kudu ya nuna wa Oscar Pistorious hoton ramin harbin bindigar da ya yi wa buduwarsa, Reeva Steenkamp amma ya ki kallo.

Kowa a kotun ya kadu yayin da mai shigar da karar ya nuna wa zakaran tseren hoton, a yayin da ya fara yi masa tambayoyi.

Lauya mai shigar da kara, Gerrie Nel ya umarci Pistorious ya kalli hoton.

Amma sai Pistorious ya kau da kansa, cikin kaduwa, ya kuma ce, ba ya bukatar kallon hoton saboda a lokacin da lamarin ya faru ya rike budurwar tasa.