Za a jinkirta wasannin Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tarin furannin da aka ajiye domin martaba magoya bayan Liverpool din da suka mutu a 1989.

Za a jinkirta wasannin a Ingila a karshen wannan makon da mintina bakwai domin karrama magoya bayan Liverpool da suka mutu a turmutsutu a 1989.

Kocin kungiyar Everton Roberto Martinez ya yaba da matakin karrama mutanen.

Ya ce, ''abu ne me muhimmanci daga dukkanin lig da kowa a fagen kwallon kafa a duniya, su martaba abin da ya faru shekaru 25 da suka wuce.''

A lokacin fara wasan kusa da karshe na kofin FA ne magoya bayan Liverpool da za ta kara da Nottingham Forest ranar 15 ga watan Afrilu na 1989 'yan kallon suka rasu a turmutsutsu.

Yanzu za a yi dukkanin wasannin manyan lig-lig takwas na Ingila da wasan Kofin FA tsakanin ranakun 11 zuwa 14 na watan Afrilunnan minti bakwai bayan lokacin farawa.