Man United za ta sayi sabbin 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za mu kashe kudin da ya kamata wajen sayen 'yan wasan da za mu samu in ji Moyes

Kociyan Man United David Moyes ya ce rashin damar zuwa gasar Zakarun Turai a kaka ta gaba ba zai hana su sayen 'yan wasan da suke shirin saya ba.

Moyes ya ce, 'yan wasan da suke sa ran saye sun san cewa rashin kungiyar gasar na wani dan gajeren lokaci ne kawai.

Kociyan ya nanat cewa, ''duk 'yan wasan da muka tuntuba a asirce suna matukar farin cikin zuwa Manchester United.''

A ranar Laraba ne Bayern Munich ta fitar da Zakarun na Premier daga gasar Zakarun Turai da ci 3-1, jumulla a karawa biyu 4-2.

Kuma kasancewar kungiyar a matsayin ta bakwai a Premier a yanzu da wuya ta samu damar zuwa gasar ta gaba ta 2014-15.