Hukumar FA ta ci tarar Jose Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lokacin da Mourinho ya fusata a wasansu da Aston Villa

An ci tarar kocin Chelsea, Jose Mourinho fan dubu 8 sannan kuma aka gargadeshi saboda korar shi da aka yi a wasansu da Aston Villa a watan da ya wuce.

Mourinho ya shiga cikin fili don magana da alkalin wasa Chris Foy bayan da aka kori Ramires daga wasan.

Ya musanta laifin da aka zargeshi da aikatawa amma kwamitin bincike ya same shi da laifi.

Mourinho ya caccaki alkalin wasan da maganganu bayan da Chelsea ta sha kashi a wajen Aston Villa da ci daya mai ban haushi.

A cewar Mourinho ya je ya gaya wa alkalin wasa Chris Foy ne cewar dan kwallon Villa Gabriel Agbonlahor wanda aka fitar daga cikin wasa, ya ture Ramires ne.

Karin bayani