Pistorius ya sha tambayoyin kwa-kwab

Hakkin mallakar hoto
Image caption Oscar Pistorius

Masu bagatar da kara sun yi wa dan tseren Afrika ta Kudun Oscar Pistorious tambayoyin kwa-kwab, a shara'ar kisan kai da ake yi masa.

Babban mai gabatar da kara, Gerrie Nel ya yi masa tambayoyi a kan irin tuka da warware da yayi a bahasin da ya bayar.

Mista Nel ya kafe ne a kan dalilin da ya sa Oscar ya yi harbi a kan kofar ban dakin gidan sa duk da cewa kofar na rufe.

Mista Nel ya kuma zargi Oscar da kin tunawa da abubuwan da ba zasu yi masa dadi ba a shara'ar tasa.

An dage shara'ar zuwa ranar litinin mai zuwa.

Karin bayani