Hankalina ya kwanta - Wenger

Image caption Yanzu za mu mayar da hanakalinmu a kan Premier in ji Wenger

Arsene Wenger ya ce hankalinsa ya dan kwanta bayan da kungiyarsa ta kai wasan karshe na kofin FA da ta fitar da Wigan.

Da wannan nasara da Arsenal ta samu a bugun fanareti 4-2 bayan sun tashi 1-1 har bayan karin lokacin fitar da gwani, ta kama hanyar sake daukan kofin tun da ta dauke shi a 2005.

Wenger , ya ce, ''na samu kwanciyar hankali sosai saboda muna cikin matsin lamba. Na yi tsammanin wasa mai wuya daman amma dai ban gamu da rashin sa'a ba.''

Arsenal wadda ta fado daga matsayin ta hudu a Premier za ta hadu da Hull City a wasan karshe na Kofin na FA.

Wenger ya kuma ce za su wuce Everton wadda ta hau matsayi na hudu a Premier, domin samun damar zuwa gasar Kofin Zakarun Turai.