Muna bayan Gerardo Martino- Puyol

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu Martino na da damar daukar kofi yayin da Barcelona za ta kara da Real Madrid a gasar Copa del Rey

Kyaftin din Barcelona ya ce, 'yan wasan kungiyar na goyon bayan kociyansu Gerardo Martino ko ta wana hali.

Puyol, ya ce, '' bana jin akwai bukatar yin wani gagarumin sauyi.

Dole ne ka samu wani tsari na aiki, ba wai kawai ta yadda za ka yi nasarar daukar kofi daya ko biyu ba.''

Martino mai shekaru 51 ya sha suka bayan ba tsammani ranar Asabar Granada ta yi galaba a kansu abin da ya jefa fatansu na daukar La Liga cikin hadari.

Barcelona ta gamu da rashin nasarar ne bayan da ta daya a La Liga Atletico Madrid ta fitar da ita a wasan dab da na kusa da karshe na Zakarun Turai.