Chelsea ta rage farashin tikiti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Chelsea a filin wasa

Kungiyar Chelsea ta rage farashin tikitin magoya bayanta da za su je wasanta da Atletico Madrid a gasar Zakarun Turai.

Ta rage fan ashirin a kan kowane tikitin shiga kallon wasan.

A cewar kungiyar matakin don karfafawa magoya bayanta gwiwa ne saboda karsashin da suke karawa kungiyar a kakar wasa ta bana.

An baiwa Chelsea tikiti 3,071 a wasan da za ta buga a Madrid a ranar 22 ga watan Afrilu.

Farashin tikitin ya soma ne daga fan 38 zuwa fan 79.50.

Karin bayani