Man City ta fi biyan 'yan wasa albashi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Toure da Aguero da Silva sun linka abin da ake biyan sauran 'yan wasan

Manchester City ce ta fi duk wata kungiyar wasanni biyan albashi mai yawa, inda 'yan wasanta da ke wasa ko da yaushe ke samun kusan Euro miliyan biyar da dubu 900 a shekara.

Real Madrid ita ce ta biyu amma a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa, inda 'yan wasanta ke karbar albashin kusan Euro miliyan biyar da rabi.

Barcelona ce ta zo ta uku a binciken wadda ita kuma 'yan wasanta ke karbar albashin kasa da Euro miliyan biyar da dubu 400.

Sai Bayern Munich 4,840,030, sai Man United 4,751,643, sai Chelsea 4,380,101, sai kuma Arsenal mai biyan Euro 4,288,906.