Crystal Palace ta doke Everton 3-2

Image caption Nasarar Crystal Palace ta taimaka wa Arsenal

Arsenal ta cigaba da zama ta hudu a Premier bayan da Everton ta sha kashi a hannun Crystal Palace da ci 2-3.

Arsenal wadda a ranar Talata ta kawar da Everton daga matsayin ta hudu tana hamayya da Everton din a wannan matsayi da bambancin maki daya.

Puncheon ne ya fara ci wa Crystal Palace kwallonta a minti na 23, sannan Dann ya kara ta biyu bayan minti 26.

Daga nan kuma sai Naismith ya rama wa Everton kwallo daya a minti na 61, kafin kuma Jerome ya kara kwallo ta uku ta Palace.

Ana sauran minti hudu lokaci ya cika sai Everton ta rama kwallo ta biyu ta hannun Mirallas.

Yanzu Everton ta ci gaba da zama ta biyar da maki 66, Arsenal na ta hudu da bambancin maki daya, yayin da Crystal Palace take matsayi na 11 da maki 40.