Gundogan ya kubuce wa Man United

Hakkin mallakar hoto v
Image caption Gundogan ya ce, ''zan yi duk abin da zan iya in taimaka wa abokan wasana nan ba da dadewa ba.''

Dan wasan Borussia Dortmund Ilkay Gundogan wanda Manchester United ke neman saya ya sabunta kwantiraginsa da kungiyar.

Dan wasan na tsakiya mai shekaru 23 da ke wa Jamus wasa ya sabunta yarjejeniyarsa ta zama a gasar ta Bundesliga har zuwa shekara ta 2016.

Gundogan wanda ba sosai ya yi wasa ba a wannan kakar ta 2013-14 saboda ciwon baya da yake fama da shi, an yi ta ba da rahotannin cewa zai koma wasu manyan kungiyoyi.

Bayan sabunta zaman nasa ya ce, ''ina matukar godiya da klub din ya ba ni damar cigaba da kasancewa da wannan kungiya ta musamman da wannan wuri na musamman.''

Dortmund na kokarin rike gwanayen 'yan wasanta, inda a makon da ya wuce ta sayi Nuri Sahin daga Real Madrid bayan zaman aron da yayi.

Sai dai za ta rasa babban dan wasanta na gaba Robert Lewandowski da zai tafi Bayern Munich a lokacin bazara.