Ba zan bar Sunderland ba - Poyet

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Gus Poyet na fuskantar matsin lamba

Kocin Sunderland, Gus Poyet ya musanta rade-radin cewar zai fice daga kungiyar wacce ke tangal-tangal a gasar Premier ta bana.

Sunderland ce ta karshe a kan teburin gasar Premier, a yayinda za ta fuskanci Manchester a filin Etihad a ranar Laraba.

Poyet mai shekaru 46 ya ce canza manaja a kungiyar ba zai warware matsalar da suke ciki ba.

"Mutane na tunanin zan fice daga kungiyar, amma ba zan fice ba," in ji Poyet.

Poyet ya kasance koci na shida a Sunderland cikin kasa da shekaru shida.

Karin bayani