Ronaldo ba zai kara da Barcelona ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cristiano Ronaldo

Dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo ba zai buga wasansu na kofin Copa del Rey ba tsakaninsu da Barcelona.

Kocin Real, Carlo Ancelotti ya tabbatar da cewar Ronaldo mai shekaru 29 na fama da ciwon kafa.

Ancelotti ya ce "Cristiano ba zai buga ba saboda bama son muyi kasada".

A ranar Laraba mai zuwa Real za ta kece raini Bayern Munich a gasar zakarun Turai.

Ronaldo bai buga wasanni Real uku a jere ba saboda rauni.

Barcelona ce ta uku a kan teburin La Liga a yayinda Atletico Madrid ke matakin na farko sai Real Madrid ta biyu.

Karin bayani