Gareth Bale na harin karin kofuna biyu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gareth Bale ya ci kwallaye 20 da suka hada da 14 na La Liga a bana

Gareth Bale na fatan ganin ya sake taimaka wa Real Madrid ta dauki karin kofuna biyu da zai kasance ta ci kofuna uku a bana bayan ta lashe kofin Copa del Rey.

Real Madrid wadda ita ce ta biyu a gasar La Liga za kuma ta yi wasan kusa da na karshe na gasar Kofin Zakarun Turai da Bayern Munich, da dan wasan ke fatan ganin sun dauki duka kofunan.

Bale dan yankin Wales mai shekaru 24, shi ne ya ci kwallo ta biyu, da ta bai wa Real Madrid damar daukar kofin na Copa del Rey a wasansu da Barcelona.

Kafin yanzu ana ganin kasawar dan wasan ta ci wa kungiyar kwallo a manyan wasanninta na fita kunya.