Giroud ya roki Manchester United

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Giroud ya ce, ''ina bukatar in yi ta cigaba da cin kwallaye''

Dan wasan Arsenal Olivier Giroud na son ganin Manchester United ta ci Everton a wasan da za su yi ranar Lahadi domin ba wa kungiyar tasa karin damar zama a matsayin ta hudu.

Dan wasan na Arsenal ya bukaci 'yan United su taimaka wa kungiyar tasa, ta hanyar doke Everton a Goodison Park.

Arsenal wadda take matsayi na hudu a Premier yanzu tana gaban Everton da maki daya ne kawai kuma za ta samu gurbin gasar Zakarun Turai idan ta ci sauran wasanninta hudu.

Giroud wanda ya ci daya daga cikin kwallaye ukun da Arsenal ta jefa ragar West Ham da hakan ya kawo kwallayen da ya ci a bana zuwa 20, ya ce yana son cigaba da cin kwallaye domin nuna kimarsa.