An zambaci Odemwingie

Hakkin mallakar hoto Phil Greig
Image caption Jami'ar ta nuna nadama tare da neman gafara kan abin da ta yi

Wata jami'a mai shirya tafiye tafiyen shakatawa da ta zambaci Peter Odemwingie na Stoke City tare da wasu mutane shida fam dubu 80 ta yi alkawarin dawo musu da kudinsu.

Jami'ar mai suna Claire Duke mai shekaru 38 ta tabbatar wa kotun da ta saurari shari'ar cewa ta zambaci mutanen bakwai ne wadanda ke mu'amulla da kamfaninta.

Daga cikin kudin, ta zambaci dan wasan dan Najeriya fan dubu 22, wanda ya biya domin saya masa tikitin jirgi da biyan wuraren shakatawa da zai je.

Kotun ta yanke wa matar hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari da aka jingine, wato za a aiwatar mata da shi a duk lokacin da aka sake samunta da wani laifi.