'Yan Liverpool na takara da juna

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sune kashin bayan Liverpool a kakar wasa ta bana

An saka sunayen 'yan wasan Liverpool Luis Suarez, Steven Gerrard da kuma Daniel Sturridge cikin jerin 'yan wasan da za baiwa kyautar gwarzon dan kwallon Premier a bana.

Kyautar ta PFA wacce kwararrun 'yan kwallo ke zaba, an saka sunayen Yaya Toure na Manchester City da Eden Hazard na Chelsea da kuma Adam Lallana na Southampton.

Tsohon dan kwallon Tottenham,Gareth Bale ne ya samu kyautar a kakar wasan da ta wuce.

Haka nan kuma an saka sunayen Sturridge da Hazard cikin wadanda za a baiwa kyautar gwarzon matasan 'yan kwallo a gasar ta Premier.

Sauran matasan da ke cikin jerin sun hada da Raheem Sterling na Liverpool da Aaron Ramsey na Arsenal da Ross Barkley na Everton da kuma Luke Shaw na Southampton.

Karin bayani