'United za ta farfado a karkashin Moyes'

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Mata tare da David Moyes

Dan kwallon da ya fi kowanne tsada a Manchester United, Juan Mata ya ce tabbas kungiyar za ta farfado a karshin jagorancin David Moyes.

Wannan ne lokaci mara dadi a tarihin United tun a shekarar 1991.

Mata ya ce "Na san cewar yanayin da muke ciki babu dadi amma dai makomar kungiyar a nan gaba nada haske".

Mata mai shekaru 25 wanda ya hade da United daga Chelsea a kan fan £37.1 a watan Junairu, na saran kungiyar za ta sayi sabbin 'yan wasa don ta farfado.

David Moyes ya maye gurbin Sir Alex Ferguson a watan Yuli, kuma kungiyar a halin yanzu ba za ta je gasar zakarun Turai ba.

Karin bayani