Wilshere zai iya zuwa Brazil - Wenger

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wilshere a lokacin da yaji rauni

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya shaidawa kocin Ingila Roy Hodgson cewar Jack Wilshere zai murmure kafin gasar cin kofin duniya da za a soma a watan Yuni.

Wilshere mai shekaru 22, yana jinyar karaya a kafarsa ne bayan da yaji rauni a ranar 5 ga watan Maris lokacin yana bugawa Ingila kwallo.

A ranar 13 ga watan Mayu, Hodgson zai fitar da jerin sunayen 'yan kwallo 30 da ake saran zai tafi da wadansu daga cikinsu zuwa gasar da za buga a Brazil.

Wenger yace "Na gaya masa cewar Wilshere zai iya buga gasar, zai iya komawa taka leda nan da makonni biyu zuwa uku".

Ingila na rukuni mai sarkakiya a gasar kofin kwallon kasashen duniya, inda za ta hadu da Italiya da Uruguay da kuma Costa Rica.

Karin bayani