Chelsea ta rike Atletico Madrid 0-0

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Chelsea ta yi wasan tsare gida

Chelsea ta rike Atletico Madrid suka ta shi canjaras ba ci a karon farko na wasan kusa da karshe na gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Duk da yadda 'yan Atletico Madrid suka samu damar rike kwallo fiye da Chelsea ba su samu damar jefa kwallon ragar bakin ba.

Minti 15 da fara wasan ne kuma mai tsaron gidan Chelsea Petr Cech ya ji rauni aka maye gurbinsa da Mark Schwarzer.

A ranar 30 ga watan nan na Afrilu ne za a yi karo na biyu na wasan a gidan Chelsea Stanford Bridge.

John Obi Mikel da Frank Lampard ba za su yi wasan na biyu ba saboda katin gargadi da aka basu, shi ma Gabi na Atletico da aka bashi katin tare da Obi ba zai yi wasan ba.

A gobe ne kuma za a yi wasa na biyu tsakanin Real Madrid Bayern Munich a Madrid.