Eto'o ba zai fuskanci Atletico Madrid ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsohon gwarzon dan kwallon Afrika, Samuel Eto'o

Samuel Eto'o ba zai buga wasan Chelsea na zagayen kusa da karshe ba a gasar zakarun Turai tsakaninsu da Atletico Madrid.

Dan kwallon Kamarun na fama da rauni a idon sawunsa a don haka bai je Spain da sauran tawagar Chelsea din ba.

Eto'o wanda ya zura kwallo daya a wasan da suka sha kashi a wajen Sunderland a ranar Asabar zai yi jinya kafin ci gaba da taka leda.

Sai dai Eden Hazard ya yi horo bayan jinyar makonni biyu da yayi.

An dakatar da Branislav Ivanovic daga buga wasan a yayin da Nemanja Matic da kuma Mohamed Salah ba za su iya buga wasan ba.

Tunda Eto'o ba zai buga wasan ba, watakila Mourinho ya zabi Fernando Torres wanda tsohon dan kwallon Atletico ne.

Karin bayani