Kevin Mirallas ya tafi doguwar jiyya

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Mirallas ya ci wa Everton kwallaye uku a wasannin hudu da suka gabata

Kevin Mirallas ba zai buga sauran wasannin wannan kakar ba saboda raunin da ya ji a matse-matsinsa a karawar da Everton ta yi da Manchester United ranar Lahadi.

Dan wasan dan kasar Belgium wanda ya ci daya daga cikin kwallaye biyun da kungiyarsa ta ci Manchester United an fitar da shi daga wasan saboda raunin a kusa da karshen wasan.

Mirallas mai shekaru 26 ba zai buga wasan Everton da Southampton da Manchester City da kuma Hull City ba.

Dan wasan wanda ya komo Everton daga Olympiakos a 2012, ya yi wasanni 37 a bana, inda ya ci kwallaye takwas.

Duk da wannan jiyya da za ta hana shi buga sauran wasannin Premier uku da suka rage, amma zai samu damar zuwa gasar cin Kofin Duniya.