An cire alamar Moyes daga Old Trafford

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tun watan Agusta aka yi kyallen

An cire kyallen nan dake dauke da alamar David Moyes a Manchester United

Kyallen wanda aka rubuta 'wanda aka zaba' dai na makale ne a filin wasa na Old Trafford tun watan Agustar bara.

Aamma an cire kyallen gabanin wasan da kulob din Man U zai taka a karshen mako tare da Norwich.

An dai yi kyallen ne bayan da Sir Alex Ferguson ya bada sunan Moyes a matsayin wanda zai gaje shi a Manchester.