Brazil 2014:Nigeria na shirin karshe

Image caption An baiwa Stephen Keshi karin lokaci domin tattara sunayen wadanda zasu je Brazil

Yayin da ya rage kwanaki 49 a tafi zuwa gasar cin kofin duniya a Brazil, Kasashen Afirka da zasu halarci gasar na cigaba da kammala shirye shirye na karshe domin zuwa wannan gasa.

An dai baiwa Kasashen da zasu je gasar wa'adin ranar 13 ga watan Mayu da su mika sunayen tawagar 'yan wasan mutum 30 da zasu je gasar ga hukumar FIFA.

An yi tsammani cewa Nigeria zata mika sunayen tawagar 'yan wasan ta ga hukumar FIFA a ranar laraba amma sai dai ta dage tura sunayen zuwa mako guda domin baiwa mai horar da 'yan wasa Stephen Keshi karin lokaci domin ya kammala hada jerin sunayen.

Masu sharhi dai na ganin hakan baya rasa nasaba da kamun kafar da 'yan wasa suke tayi domin ganin cewar sun sami shiga.