" 'Yan Real Madrid sun bani mamaki"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arjen Robben

Dan kwallon Bayern Munich Arjen Robben ya ce ya sha mamakin yadda Real Madrid ta buga kwallo a wasansu na gasar Zakarun Turai.

An tashi Real Madrid na da ci daya, Bayern na nema, duk da cewar 'yan Bayern dinne suka shafa leda.

Robben ya ce "Na saran Real za su fito su murza leda amma sai suka kasance a baya".

Karim Benzema ne ya kwallon da ya baiwa Real nasara a kan Beyern.

Kocin Bayern, Pep Guardiola ya jinjinawa 'yan wasansa inda ya ce za su farke a wasa na biyu da za a buga a Jamus.

A ranar Talata mai zuwa ne Bayern Munich za ta bakunci a filin Allian Arena.

Karin bayani