Newcastle na bukatar karin 'yan kwallo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shola Ameobi

Dan kwallon Newcastle Shola Ameobi ya kare kocinsa Alan Pardew, inda ya ce kungiyar na bukatar karin 'yan kwallo.

Newscastle na fama da matsala inda ta sha kashi a wasanninta biyar na gasar Premier a jere, kuma wasanni hudu kadai ta samu galaba tun karshen watan Disambar bara.

Ameobi ya ce "Muna bukatar kwararrun 'yan kwallo wadanda za su karawa tawagarmu karfi".

A cewarsa hakan ne zai sa kungiyar ta fito da karfinta a kakar wasa mai zuwa.

Ameobi wanda ya shafe shekaru 14 a Newcastle, kwangilarsa da kungiyar za ta kare ne a karshen kakar wasa ta bana.

Karin bayani