Batun United a kai kasuwa - Ancelotti

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ancelloti da mataimakinsa Zidane

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce abun dariya ne batun cewar zai koma jagorancin Manchester United.

Dan Italiya mai shekaru 54, ya kasance cikin wadanda ake dangantasu da United tun bayan da aka kori David Moyes a ranar Talata.

Ancelotti ya ce "Ina jin dadin aiki a nan kuma na yi sa'ar aiki a kungiyar da ta fi kowacce a duniya."

Tsohon kocin AC Milan din wanda ya koma Real a farkon kakar wasa ta bana, ya shafe shekaru biyu a Chelsea inda ya lashe kofin gasar Premier da na FA a kakar wasan 2009- 2010.

Karin bayani