Ba zan koma Man United ba- Klopp

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Klopp na haskakawa a Dortmund

Kocin Borussia Dortmund Jurgen Klopp ya ce ba ya son ya zama kocin tawagar Manchester United a kakar wasa mai zuwa.

Dan shekaru 46, Klopp ya kasance daya daga cikin mutanen da ake hasashen zai maye gurbin David Moyes wanda aka kora a United a ranar Talata.

Klopp yace "Babu dadi mutum ya guji wani amma dai bani da wata hujja ta barin kungiyar da nake a yanzu".

Klopp ya lashe gasar Bundesliga sau biyu tun bayan da ya maye gurbin Thomas Doll a Dortmund a shekara ta 2008.

Sannan a kakar wasan da ta wuce ya jagoranci kungiyar zuwa wasan karshe na gasar Zakarun Turai a kakar wasan da ta wuce.

Ana alakanta shi da koma wa Barcelona a kakar wasa mai zuwa amma ya ce "kada kowa ya damu a kan batun barin Dortmund".

Karin bayani