An fitar da jadawalin cin Kofin Afrika

Image caption Kasashe tara ne daga 28 da ke cikin jadawalin za su can-canci shiga gasar ta cin Kofin na Afrika.

Hukumar kwallon kafa ta Afrika, CAF ta fitar da jadawalin wasannin neman zuwa gasar cin Kofin Afrika na 2015 da za a yi a Morocco.

A rukunin A, Najeriya za ta hadu da Afrika ta Kudu da Sudan da wadda ta yi nasara a wasa na 37/38

Rukunin B ya kunshi Mali da Algeria da Ethiopia da kasar da za ta yi nasara a wasa na 43/44.

Burkina Faso da Angola da Gabon da wadda za ta yi nasara a wasa na 33/34 suna rukuni na C.

A rukunin D kuwa akwai Ivory Coast da Kamaru da Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo da wadda za ta yi nasara a wasa na 41/42.

A rukunin E za a yi fafatawar Afrika ta Yamma tsakanin Ghana da Togo da Guinea da wadda za ta yi nasara a wasa na 35/36.

Zambia da Cape Verde da Niger da mai nasara a wasa na 45/46 za su fafata a rukunin F.

Rukunin G, wanda aka yi wa lakabi da rukunin mutuwa ya kunshi Tunisia da Masar da Senegal da wadda za ta yi nasara a wasa na 39/40.

Fitaccen kociyan Masar Hassan Shehata shi ne ya jagoranci fitar da jadawalin gasar.

Za a yi gasar ne daga ranar 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga Fabrairu na 2015 a Morocco.

Moroko mai masaukin baki ta samu shiga gasar wadda za a yi bikin bude ta a birnin Marrakech kai tsaye.