Man City ta buge Crystal Palace 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Da wannan nasara da kuma rashin nasarar Liverpool Manchester City ta sake samun damar daukar Premier

Yaya Toure ya taimaka wa Man City ta yi nasara a Crystal Palace 2-0, nasarar da ta matso da kungiyar kusa da ta daya Liverpool.

Edin Dzeko ne ya fara jefa kwallo a ragar Palace bayan da Toure ya aika masa da kwallon minti hudu da shiga fili.

Minti biyu kafin tafiya hutun rabin lokaci ne kuma sai shi ma Toure ya ci tasa kwallon.

City ce ta uku yanzu a tebur da kwantan wasa daya kuma maki uku ne tsakaninta da Liverpool ta daya mai maki 80.

Chelsea kuma na matsayi na biyu da maki 78, a wasanni 36