Chelsea ta yi wa Liverpool nakasu da 2-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelse ta rage ratar da ke tsakaninta da Liverpool ta daya a Premier da maki biyu.

Chelsea ta kawo wa fatan Liverpool na daukar kofin Premier na farko a shekaru 24 nakasu, ita kuma ta kara damarta da ci 2-0.

Chelsea ta shiga gaba a wasan da aka yi a gidan Liverpool, Anfield, a minti na 45 inda Demba Ba ya jefa kwallo a raga.

Ba ya samu damar ne baya da santsi ya kwashi Steven Gerrard shi kuma ya zari kwallon har sai da ya dangana da raga.

Joe Allen da Luis Suarez sun yi ta kai hare-haren ramawa amma ba su yi nasara ba.

Ana gab da tashi ne kuma bayan mintina 90 na wasan Torres ya tsinke da kwallo ton daga tsakiya, Willian na gefensa ya ba shi ya jefa ta raga.

Karin bayani