Sunderland ta doke Cardiff 4-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nasarar ta ceto Sunderland daga rukunin faduwa daga Premier ta kuma jefa Cardiff ciki.

Sunderland ta lallasa Cardiff 4-0 ta fito daga rukunin faduwa daga Premier, ta kuma tura bakin nata cikin wannan rukuni.

Connor Wickham ne ya fara sa masu masaukin bakin gaba da ya jefa kwallo a raga daga wata kwana da aka dauko.

A minti na 45 kuma Sunderland ta samu kwallonta ta biyu da bugun fanareti ta hannun Fabio Borini, bayan Juan Cala wanda aka kora ya yi wa Wickham keta.

Wickham ya sake cin kwallonsa ta biyu kuma ta hudu ga Sunderland a minti na 86.

Yanzu Sunderland din ce ta 17 a tebur da maki 32 amma tana da kwantan wasa daya.

Cardiff ta karshe a tebur ita ce ta fi kowace kungiya rashin nasara a wasanninta na waje kuma damarta ta tsira a Premier na da wuya.