Suarez ya zama gwarzo a Ingila

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Luis Suarez da Eden Hazard

An bayyana dan kwallon Liverpool, Luis Suarez a matsayin gwarzon dan kwallon Premier na bana da kungiyar kwararrun 'yan kwallo ke bayarwa a duk shekara.

An yi bukin bada kyautar a birnin London a ranar Lahadi jim kadan bayan da Chelsea ta doke Liverpool da ci biyu da nema.

Dan kwallon Uruguay din mai shekaru 27 ya doke Daniel Sturridge don samun kyautar.

Suarez yace "Gasar Premier a cike da zaratan 'yan wasa na ji dadi da aka bani wannan kyautar".

Shi kuma dan kwallon Chelsea, Eden Hazard an zabe shi a matsayin gwarzon matasan 'yan kwallo na bana.

Tawagar Premier ta bana: Petr Cech (Chelsea), Luke Shaw (Southampton), Vincent Kompany (Man City), Gary Cahill (Chelsea), Seamus Coleman (Everton), Eden Hazard (Chelsea), Yaya Toure (Man City), Steven Gerrard (Liverpool), Adam Lallana (Southampton), Luis Suarez (Liverpool), Daniel Sturridge (Liverpool).

Karin bayani