Tottenham na neman kocin Ajax

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Mayu de Boer ya sabunta kwantiraginsa da Ajax har zuwa 2017

Zakarun Holland Ajax sun bayyana cewa kungiyar Tottenham ta tuntube su kan bukatar neman kocinsu Frank de Boer.

Kakakin kungiyar ta Amsterdam ya sheda wa BBC cewaTottenham ta tuntubi daraktanta na kwallon kafa Marc Overmars a watan da ya gabata game da kocin.

De Boer mai shekaru 43 yana daukar lig din kasar a duk shekara a shekaru hudun da ya kama aiki da Ajax.

Tottenham ta ki cewa komi kan lamarin amma za ta duba cigaban kocinta Tim Sherwood wanda kwantiraginsa zai kai har 2014-15 a karshen kakarnan.

Tsohon dan wasan bayan na Ajax da Holland wanda a ranar Lahadi ya sake daukar kofin Lig din kasar ya ce zai tattauna da Tottenham kan neman nasa, sannan kuma ya bayyana matsayinsa daga baya.