UEFA:Man City da PSG sun saba ka'ida

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban UEFA, Michel Platini

Za a iya hukunta kungiyoyin Manchester City da Paris St-Germain saboda saba ka'idar UEFA kan batun kashe kudade wajen siyo 'yan kwallo.

Kungiyoyi kasa da 20 ne suka kasa cimma ka'idar da Hukumar kwallon kafar ta Turai, UEFA, ta kafa kan batun.

A yanzu dai kungiyar Manchester City za ta zabi ko a yi mata sassauci a wajen hukunci ko kuma a hana ta buga gasar kwallon Turai a kakar wasa mai zuwa.

A ranar Juma'a UEFA za ta bayyana hukuncin da za ta dauka kan kowacce kungiya da ta saba ka'idar.

Sai dai Shugaban UEFA Michel Platini ya ce ba ya tunanin za a hana kungiyar da ta saba ka'ida shiga gasar kwallon Turai.

Karin bayani