Mourinho ya yi raddi ga masu sukarsa

Mourinho yana raddi ga masu sukar salonsa Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mourinho ya ce iya tsare gida, shi ne kwallon kafa

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya maida martani ga masu sharhi da ke sukar lamirin salon kare kai da yake amfani da shi bayan canjaras din da kungiyar ta yi da Atletico Madrid a gasar zakarun Turai da kuma wasan 2-0 da Chelsea ta doke Liverpool.

Mourinho ya ce, "Wasan kwallon kafa cike yake da 'yan ba-ni-na-iya wadanda sun fi ni fahimta, sai dai maganar gaskiya duk kungiyar da ba ta iya tsare gidanta sosai ba, a ganina ba ta da yiwuwar samun nasara."

Kocin, mai shekaru 51, ka iya lashe gasar zakarun Turai karo na uku da kungiyoyi daban-daban da ya rike, idan Chelsea ta iya buge Atletico a zagaye na-biyu na wasan kusa da na karshe a filin Stamford Bridge ranar laraba.

A zagayen farko na wasan Atletico, kungiyarsa tana da kididdigar rike kwallo kaso 31 cikin 100, yayin karawa da Liverpool kuma ranar lahadi, Chelsea na da kaso 27 cikin 100 na kididdigar rike kwallo, lamarin da ya sa kocin Liverpool, Brendan Rodgers ya yi ikirarin cewa Chelsea ta yi amfani da salon rubdugu don hana kungiyarsa cin kwallo.